By: Baban Manar Alkhasim.
بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل وسلم على محمد وآله وصحبه ومن تبعهم بالإحسان الى يوم الدين.
'Yan uwana musulmi, wannan sabon darasi ne, me yiwuwa ya dan bambanta da sauran kadan ta 6angaren aiki da hakali, ina buqatarka dan uwa, wanda Allah SW ya halicce ka da hankali ya kuma ba ka daman neman ilimi don ya bambanta ka da sauran dabbobi, da ka ba ni hankalinka kadan don mu duba inda gaskiyar take.
Lokacin da Allah SW ya yi niyyar aiko Annabi SAW duk duniya ta saki addininta, Banu Isra'ila wasu sun bar koyarwar Annabi Musa sun bi Yahudanci, Nasaran da suka kar6i addinin Annabi Isa AS suma sun canja littafin kamar dai yadda Allah SW yake cewa:
يحرفون كلم عن مواضعه.
Suna canja kalmomi daga asalin yadda suke.
Don haka zuwan Annabi SAW bai tsaya ga Larabawa ba kadai, wadan da suka saki addinin Annabi Ibrahim wato muslunci, suka dauki sabon addinin da Amr bn Lu'ay ya zo musu da shi daga qasashen Sham, har duniya gaba daya dole ta karyo kai zuwa ga Annabi Muhammad domin komowa zuwa ga muslunci,
Sai Allah SW ya turo Annabi SAW da saqo, shi kadai ne bai hada shi da kowa ba, ba kuma wani manzo kusa da zamaninsa a duk al'ummar duniya, ba kamar Banu Isra'ila ba da Annabawan ke bibiyar juna ko su zo a lokaci guda, Annabi Ibrahim da 'ya'yansa Biyu Isma'eel da Is'haq da jikansa Ya'qub da tatta6a kunnensa Yusuf AS duk manzanni ne bayansu kuma, Musa, Haroun, Shu'aib da Khidir duk zamani Daya suka yi da Thulkifl da Yusha' AS, sai kuma Dawoud da dansa Suleiman AS, suka yi zamani Daya, Zakariyya da dansa Yahya da Isa AS duk zamani Daya suka yi, Annabi SAW shi kadai ya zo shi Daya zuwa ga duniya gaba Daya ba kamar wadancan manzanni da aka aiko su zuwa ga Banu Isra'ila kadai ba.
Annabi yana kar6an wannan saqo Abubakar RA ya muslunta ba tare da wa'azi ko jinjiki ba, ya kar6i addinin ya yi watsi da wanda tun yana yaro yake ciki, haka ya lazimci Annabi SAW har Qur'ani ya sifanta shi da:
ثاني اثنين إذهما في الغار إذ يقول لصاحبه لا تحزن إن الله معنا.
Dayan mutum Biyu yayin da suke cikin kogo, lokacin da yake cewa abokinsa kada ka damu haqiqa Allah yana tare da mu.
Abubakar ya yi dace da sahibantan Annabi SAW a cikin lamarin risala, in da Annabi ya dauke shi suka bar garin Makka tare.
Abin kula a nan, me ya sa Annabi ya dauke shi, mu ahlus sunna mun ce, ba bu kamarsa a wannan lokacin, kuma shi ne ya cancanci wannan matsayin sai Annabi ya za6o shi, Allah SW ba zai bar Annabi ya yi kuskuren za6en wanda zai taimake shi isar da saqo ba, mun yi Imanin cewa Allah yana sane da Abubakar RA tun kafin ya halicce shi, da abin da zai yi har mutuwarsa don haka ya bar Annabinsa da shi.
Mai hankali zan so ka taya ni wannan hukuncin, saninka ne cewa Annabi SAW ya yi niyyar fita zuwa Madina, wanda wannan tafiya mai matuqar mahimmanci ce a tarihi da addini, tafiya ce da take nuna tashin muslunci a hukumance daga mahaifar Annabi Makka zuwa Madina, mai ya sa bai dauki Aliy RA ba sun tafi tare tunda yana da masaniyar cewa shi ne Khalifansa a bayansa?
Mai yiwuwa amsar ta zama cewa: Aliy RA ya riqi wani matsayi ne mai girma, mai matuqar wahala da hatsari, na fuskantar mutuwa daga abokan gaba, ta yadda ya kwanta a makwancin Annabi SAW, wanda da kafurai sun zo da sun kashe shi, sabo da shi kadai ne ba zai iya fuskantar garin Makka gaba daya ba.
To ma iya cewa Annabi ya kai khalifansa in da za a kashe shi kenan don ya ba Abubakar RA daman hawa khilafa? Amsar za ta iya zama a'a ai shi sadauki ne kuma Annabin yana sane da cewa kafuran ba su isa su ta6a shi ba Allah zai kare shi.
In dai amsar ta fito a haka to ba maganar tsoro ko hatsari, Allah yana tare da shi zai kare shi, amma tun da ya zama Annabi bai fita a fili zuwa Madina ba, sai da daddare kuma a bayan idon jama'a, har suka shiga kogon dutse, lallai wurin akwai hatsari, nan ne ya kamata sadauki ya yi aiki, to sai Annabi ya bar Aliy RA a wurin da ya san babu hatsari, duk da jarumtarsa da ake fadi, ya dauki Abubakar suka fita, sabo da saninsa da kuma amincewa da qudurarsa, tun da Allah ya umurce shi da fita ba zai bar Annabinsa ya yi kuskure wajen daukan abokin tafiya a wuri mai mahimmanci irin wannan ba.
Idan muka lura da kyau za mu ga cewa Annabi SAW cewa ya yi لا تحزن. "Kar ka damu" ba. لا تخف ba wato "kar ka ji tsoro" Abubakar RA duban halin da Annabi yake ciki ne shi ya sa ya ce kada ka damu Allah zai tsare mu, ya san ba tsoro a zuciyarsa da ya ce kada ka ji tsoro.
Haka Annabi SAW ya lazimci Abubakar RA har rasuwarsa, Qur'ani bai bar wani munafuki ba sai da ya tona shi, wajibin Annabi ne kuwa ya isar da saqo, ya fallasa duk wani munafuki.
Amma Annabi sai ya auri 'yar Abubakar RA wato A'ishah RA, alaqar ta dada qarfi, bayan rasuwar Annabi SAW, Abubakar ya yaqi 'yan ridda dole suka shiga muslunci, kenan hankali ba zai dauka ba a ce shi ma ya yi ridda kuma yake yaqin 'yan ridda, sannan ya kuma fara bude qasashen shi'a har mutuwa ta same shi, kenan bai bar abin da Annabi SAW ya dauko ba. Za mu duba maganar wasiyya da kai, kai kuma sai ka yi tunani.
A kan wannan ga6ar za mu ci gaba InshaAllah.
Like us on Facebook
No comments:
Post a Comment