Yau za mu duba wani babban lamari ne ni da kai, domin a ranar Litini 29/02/0011 AH, Annabi ya fara rashin lafiya, bayan ya dawo daga janaza a maqabartar Baqi, a ranar Laraba wato kafin rasuwarsa da kwana Biyar, jikinsa ya dada daukan zafi matuqa, har ya yi ta wasiyya kan kar a bauta wa qabarinsa.
A ranar Alhamis, gabanin rasuwarsa da kwana Hudu, ranar ce cutar ta yi tsanani sosan gaske, kuma ranar ce ya ce a kawo takarda ya rubuta abin da in suka riqe shi ba za su 6ata ba har abada, Umar RA ya ce, akwai fa Qur'ani tare da ku, jikin ne ya matsa masa, a nan karatunmu na 3-4 zai fito in da Allah SW ya fadi a Qur'ani cewa addini ya cika ba saura, sannan in akwai lamarin Imamanci to sai Annabi ya qi fadi sai jiki ya yi tsanani zai rasu?
Annabi ya yi umurni da Abubakar RA ya jagoranci mutane sallah bayan Aliy RA yananan a gabansa, Mai hankali kar ka manta, ya jagoranci aikin haji a baya, yanzu ga shi Annabi SAW ya sake ba shi limanci a masallacinsa wanda ba wanda ya ta6a ba shi sai shi, Abubakar ne ya yi ta sallah har Annabi SAW ya bar duniya, bai canza wani ba.
A ranar Asabar, wato gabanin rasuwarsa da kwana Biyu yadan ji sauqi ya fita sallar Azahar alhali Abubakar RA yana limanci, sai ya nemi ya ja da baya, Annabi ya umurce shi ya tsaya a in da yake, sai ya riqa koyi da Annabi, wato mutum Biyu kenan a gaba, Annabi SAW da Abubakar RA, don Allah in da wani saqo da bai isar ba? Shin yanzu ba lokacin magana ba ne? Shin ina jarumtakar Aliy RA take idan har ba zai iya tsayawa kan abar Annabi ya fadi abin da aka aiko shi da shi ba? Ko dai ana zargin Annabi ne da tsoro, ta yanda ya qi fadin saqon Allah sabo da Umar ko Abubakar RA?
A ranar Lahadi, kafin rasuwar Annabi da kwana Daya, ya yi sadaka da dinari Bakwai, ya 'yanta bayinsa, ya yi kyauta da makaminsa amma bai rubuta wata wasiya ba, bai kuma fada ba, kenan zafin jikin ranar Alhamis ya tabbata, tun da yanzu ya murmure amma bai sake maganar ba.
A ranar qarshe Abubakar RA yana sallar Asuba da mutane Annabi ya yaye labulen windo daga dakin A'ishah ya leqo su ya yi murmushi, har mutane suka kusa fitunuwa a sallah sabo da murna suna zaton zai fito ne, Abubakar RA ya fara qoqarin dawowa baya, Annabi SAW ya nuna masa hannu cewa ya cika sallarsa, har hantsi ya daga Annabi ya bar duniya bayyi wata maganar wasiyya ba, yanzu Mai hankali me za ka ce?
Mai hankali ina so ka fahimci cewa, duk fa gabar da ake qoqari a shigo da ita tsakanin sahabbannan qarya ake yi,Qur'ani da sunna da marubutan shi'a na farko duk sun tabbatar da cewa sahabbai suna qaunar junansu, ba wata gaba da take tsakaninsu har suka bar duniya, Allah SW ya ce:
محمد رسول الله والذين معه أشداء على الكفار رحماء بينهم...
Muhammad dan saqon Allah ne, wadan da ke tare da shi masu tsananta wa kafurai ne da tausayawa a tsakaninsu.
Al Fat'hu 29
Za mu ga yadda Annabi ya auri 'yar Abubakar da Umar RA, Usman RA ya auri 'ya'yan Annabi guda Biyu, Aliy RA ya auri 'yar Annabi SAW, Umar RA ya auri 'yar Aliy RA duk wannan yana nuna qaunar da take tsakanin wadannan Khalifofin ne, domin auren Umar RA da 'yar Aliy RA bai kasance ba sai bayan rasuwan Annabi, kenan duk abin da ake fadi qarya ne kawai da canza tarihi.
Malaman shi'a suke cewa:
أنس رض قال قال لي النبي ص: انطلق فادع لي أبابكر وعمر وعثمان وطلحة والزبير وبعدد من الأنصار•قال: فانطلقت فدعوتهم له فلما أخذوا مجالسهم قال: ...إني أشهدكم أني قد زوجت فاطمة من علي على أربعمائةمثقال من فضة.
Anas RA ya ce Annabi SAW ya ce masa tafi ka kirawo Abubakar, Umar, Usman, Talhah, Zubair da wasu mutanen madina da dama. Ya ce sai na tafi na kirawo su, yayin da suka sami wuri suka zauna ya ce: Ku shaida cewa na aurar da Fatimah ga Aliy akan kwatankwacin azurfa 400.
Kashful Gumma 1/358. Bihar 43/119
Sannan hatta auren, lokacin da Aliyun RA bai da sadaki Annabi SAW ya ce sai dai ya sayar da sulkensa, haka ya dauka ya tafi wuri Usman RA, Usman ya kar6i sulken ya ba shi kudin, sannan ya mayarmasa da sulken a matsayin gudummuwarsa, da Aliy RA ya kawo kudin, Annabi SAW ya ba Abubakar RA kudin ya ce ya je ya siyo mata kayan daki.
Kashful Gumma 1/369. Bihar 43/130
Wadannan duk littafan shi'a ne suke bayyana qaunar da take tsakanin wadannan sahabban, na soyayya da qaunar juna, amma ba abin da suke koyar da dalibansu ba kenan, yanzu mu duba yadda Usman RA ya yi, a maimakon ya ba da kudin a matsayin sadaki a ce shi ya biya, sai ya sayi sulken da kudin da zai kai sadakin, don ya zama Aliy RA ya biya sadakin da guminsa, sannan ya mayar masa da sulkensa a matsayin gudummuwa, kuma ku duba wanda aka ba shi alhakin sayo kayan daki gaba daya, Abubakar ne RA, ku duba shedun da aka kira, wadannan su ne 'yan shi'a suke tsine musu kullun.
Mai hankali wadannan fa littafan shi'a ne, da za mu dauko littafan sunna ya kake zaton za mu bayyana abin? Shin me ya sa malaman shi'a ba sa koyar da dalibansu irin wadannan halayya da dabi'u masu dadi sai nuna gaba da tsinuwa ko da yaushe?
Like us on Facebook
No comments:
Post a Comment