Tuesday, 3 December 2013

MAI HANKALI YI TUNANI! 2.

By; Baban Manar Alqasim

بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل وسلم على نبيك محمد وآله وصحبه وسلم.

Mai hankali dan taimake ni duba wannan lamarin: Annabi SAW shi ne da kansa yake wakiltar Sahabbansa gaba Daya a duk aikin Haji wanda shi ma ginshiqi ne daga shika-shikan muslunci, amma a shekara ta Tara bayan Hijira sai ya tura Abubakar RA da ya na'ibance shi, ya jagoranci jama'a, a Daya daga cikin rukunan muslunci wanda dukkan musulmai za su dawo qarqashinsa ne, shi ne mai umurni da hani a matsayin jagora, har sai da ayar warware duk ittafaqin da musulmai suka rattaba hannu ta sauka, wace Annabi SAW ya tura Aliy RA da ita da cewa ya bi Abubakar RA ya karanta wa musulmai a matsayinsa na dan saqo.

A wannan shekarar, Abubakar ya zartar da hukuncin cewa babu sauran bautar gumaka a yankin Larabawa gaba Daya, tun daga wannan ranar, shin hankali zai dauka a ce kuma ya riqa bauta musu a 6oye, sannan Allah bai gaya wa Annabinsa ba, har ya jagoranci mutane a irin wannan matsayi na jagorancin duniya? Wani irin qwaqwalwa ce wannan? A wannan lokacin ne fa Abubakar RA ya hana duk wani mushriki dawafi, ta ina za a sifanta shi da wannan in an so adalci?

A shekara ta Goma Annabi ya yi Hajjin ban kwana mai ban tausayi, wanda bayansa ba a sake yi da shi ba, sai Abubakar RA ya ci gaba da jagorantar aikin haji a matsayinsa na Khalifa bayan Annabi, kenan kamar Annabin ya koyar da shi ne tare da nuna wa duniya matsayinsa a harkar addini, a wannan lokaci ne Annabi ya yi bayani dalla-dalla game da abubuwan da suka shafi addini manya da qanana, amma sam bai yi maganar Imama ko Wilaya ko Wasiyya da 'yan shi'a suke zaluntar muslunci da shi ba, su ma ba su yi da'awar cewa ya yi ba, har ayar qarshe ta sauka wa Annabi cewa:
اليوم أكملت لكم دينكم وأتممت عليكم نعمتي ورضيت لكم الإسلام دينا.
A yau dinnan na kammala muku addininku, na cika muku ni'imata, na amince muku cewa muslunci shi ne kadai addini.

Mas'aloli masu mahimmanci su ne: In dai har akwai maganar wasiyya, Annabi bai riga ya isar ba bayan duk Annabawa sun san da ita, ta ya Allah SW zai saukar da cewa addini ya cika? Musulmi ba zai ce Allah SW bai san cewa Annabi bai isar da wasiyya ba, matuqar akwai ta. To sai dai a ce ai lokacin maganar wasicin ba ta zo ba, da Annabi ya isar a wurin, wannan ya sa6a wa aqidar shi'a gaba Daya, don Annabi wai tun aiko shi yana sane da khalifancin Aliy RA, bal duk manzanni ma sun sani, to a nan wa za a zarga? Kowanne zargi a ciki kafurci ne.

Dan uwa musulmi, baka da bukatar wahal da kanka, ko ba ka da ilimi ka san cewa, maganar wasicinnan dama ce da za a zargi Annabi SAW da rashin isar da saqo gaba Daya, don kuma bai ta6a maganar wasici ba ko khalifancin Aliy RA, ta ya sai ya zo rasuwa ne zai yi???

Mai hankali dan saurare ni kadan! A sama na  kawo ayar da take tabbatar da cewa Annabi Muhammad SAW ya isar da saqo:
اليوم أكملت لكم دينكم وأتممت عليكم نعمتي ورضيت لكم الإسلام دينا.
A yau dinnan na kammala muku addininku. Na cika muku ni'imata, na amince muku cewa muslunci shi ne kadai addini.
Ma'ida aya ta 3

Wannan ya nuna babu wani zancen Imama wanda Annabi bai isar ba, sai dai in za a zarge shi da 6oye saqon da Allah ya yi masa, ko a qaryata ayar Qur'ani, koda yake kai mai hankali ka san cewa ba yadda za a yi Annabi SA ya 6oye wani abu bai isar ba a matsayin manzo kuma Allah SW ya qyale shi, to mu ahlus sunna mun yi imani cewa Annabi ya isar da duk saqon da aka yi masa, maganar imamanci da bai fadi ba dama ba muslunci ba ne da ya isar.

Khumaini yake cewa:
وواضح أن النبي لو كان قد بلغ بأمر الإمامة طبقا لما أمر به الله وبذل المساعي في هذا المجال لما نشبت في البلدان الإسلامية كل هذه الاختلافات والمشاهنات والمعارك ولما ظهرت ثمة خلافات في أصول الدين وفروعه.
A sarari yake cewa da Annabi ya isar da lamarin Imama kamar yadda Allah ya umurce shi, kuma ya zage dantse a kan haka, da duk wadannan sa6anin da tashin-tashina da rikice-rikicen da suke faruwa a qasashen muslunci ba su faru ba, kuma da ba a sami wani sa6ani a Tauhidi da Fiqihu ba.
Kashful Asrar na Khumaini.

Ya fito sarari kenan dama Annabi suke so su zarga da cewa bai isar da saqon da Allah ya yi masa ba, in kuwa za su yi wa Annabi haka, haqiqa Abubakar da Umar RA ba tsira za su yi ba, don sun zarge su da hana wasiya, mai hankali kar ka yi zaton Annabi ne kadai suke zargi a'a hatta sauran Annabawan dubi abin da Khumaini yake cewa a wata huduba da ya yi ta tunawa da haihuwar Mahadi a ranar 15 Sha'aban 1400 AH:

لقد جاء الأنبياء جميعا من أجل إرساء قواعد العدالة في العالم لكنهم لم ينجوا حتى النبي محمد خاتم الأنبياء الذي جاء لإصلاح البشرية وتنفيذ العدالة لم ينجح في ذلك.
Annabawa gaba dayansu sun zo ne don saka ginshiqai na adalci a bayan qasa, sai dai sun gaza yin hakan, hatta Muhannad, cikamakon Annabawa da ya zo domin gyara dan adam da zartar da adalci ya gaza yin hakan.
Ka duba Nahaju Khumainiy p46

Wannan ya nuna cewa suna da tabbacin cewa Annabi bai bar wata wasiyya da zata tabbatar da cewa Aliy RA shi ne khalifa bayan Annabi ba, to mai hankali wanda zai furta irin wandannan kalaman ga Annabin rahama kana ganin zai qyale sahabbansa?

No comments:

Post a Comment