Thursday, 19 December 2013

MAI HANKALI YI TUNANI! 5

By:  Baban Manar Alkhasim

Mai hankali, saninka ne cewa dukiyar Abubakar ce ta farkon da aka fara aiki da ita wurin daukaka kalmar Allah bayan ta Khadijah RA, sannan saninka ka ne cewa ya rasu a talakansa ne ba kamar yadda ya shiga muslunci ba, sa6anin shugaban 'yan gwagwarmayan Nigeria, da ya shiga a talakansa yanzu yana hawa manyan motoci ga makadeden gida ga maqudan kudi a banki.

Bayan rasuwar Annabi SAW Abubakar RA ya ci gaba da jagorancin musulmai da bude qasashe ana yada muslunci, wanda wannan ne Annabi SAW yake yi, ba wani abu da Abubakar ya qara ko ya rage, kamar dai yadda ya fadi a hudubarsa cewa a yi masa biyayya matuqar ya bi umurnin Allah, sannan a sa6a masa matuqar ya sa6a wa umurnin Allah, Abubakar ya ba da 'yancin a yi fito na fito da shi matuqar ba shi a kan daidai, kenan shurun da Aliy RA ya yi, da rashin fuskantar Abubakar RA game da sha'anin khalifanci yana nuna gamsuwarsa da lamarin.

Zancen 'yan ridda da Abubakar RA ya yaqa ba kashi Daya ba ne, 'yan shi'a suna qoqarin nuna cewa Abubakar RA ya yaqi wadan da suka sa6a masa ne a siyasarsa alhali wannan qage ne na masamman, akwai qabilu da suka yi ridda kowanne da dalilinsa: Banu Asad da Gatfan, Banu Kinda, Banu Mazhaj, Banu Hanifa, Banu Sulaim, Banu Tameem.

Sabbin shiga muslunci wadan da imani bai gama ratsa zukatansu ba, ba shakka dukiyarsu ta fi musu musluncin, shi ya sa Annabi na rasuwa suka ce ba za su ba da zakka ba, wace rukuni ce daga cikin rukunnan muslunci, Abubakar ya nemi su juyo zuwa ga addini ko a saka su dole, suka za6i yaqi, aka yaqe su, aka musluntar da su dole, akwai Al'Aswadul Unsiy ya yi ridda tun Annabi bai bar duniya ba ya koma Yemen tare da sojojinsa su 700, Abubakar ya yake su.

Akwai wadan da suka yi da'awar Annabci, ciki harda Aswad din da Musailama da Sujahut Tamimiyya,duk wadannan Abubakar RA ya yaqe su ya dawo da kalma ta zamo guda Daya, sannan akwai mutanen Baharain da suka ce tun da fa Annabi SAW ya rasu to ba su ba muslunci domin da shi Annabi ne da bai rasu ba, wadannan sun yi ridda gaba dayansu in ba wani qauye da ake kira Juwaathaa'u ba, haka Abubakar ya yaqe su ya sa suka dawo muslunci.

Abubakar RA bai fara yada muslunci ba sai da ya tabbatar kan Al'umma ya dawo ya sake dinkewa kamar yadda Annabi SAW ya bar shi, daga nan ya fara bude qasashen da shi'a suke a yau, ba shakka har Annabi ya rasu suna kafurcinsu ne, ba su san muslunci ba sai Khalifancin Abubakar wanda yau suke cewa kafuri ne bayan ya musluntar da su, ya bude Iraqi da qasashen Sham Allah ya qara yadda a gare shi.

Mai hankali ina so yau mu duba wasu lamarori ne masu mahimmanci ni da kai, ka san dai mun gabatar da rayuwar Abubakar RA yadda ya yi ta da Annabi SAW, da abin da muka fitar a ciki na ilimi wanda hankalinka zai tabbatar maka da yadda rayuwar take, to ya matsayin Abubakar a wurin 'yan shi'an yanzu?

Shi'an yanzu suka ce: Abubakar ya qi fadin kalmar shahada lokacin rasuwarsa, ya bayyana da kansa cewa zai shiga (Wani akwati na wuta, wanda aka kulle yake da kwadon wuta, a ciki akwai mutum 12 da ni da wannan abokin nawa, na ce Umar ya ce: Qwarai, da kuma wawukeken rami na Jahannama da wani dutse a samansa idan Ubangiji yana son ya hura wutar sai ya daga dutsen.
Sulaim bin Qais p208 Ba'du aqwali Muhammad bn Abibakr Bugun Darul irshad. Bihaar 30/131 Babu ma azhara Abubakr wa Umar.

Asafwil Jaza'iriy yace:
إن أبابكر كان يصلي خلف رسول الله ص والصنم معلق في عنقه وسجوده عليه.
Haqiqa Abubakr ya riqa salla a bayan Annabi SAW alhali akwai gunki a rataye da wuyarsa, a kansa yake sujjada.
Al'anwarul Nu'maniyya 1/53. Nur Murtadwiy,
Hatta yaqin 'yan ridda da ya yi sai da suka ce
فكان هذا الفعل منه فعلا فظيعا، وظلما عظيما، وتعديا بينا.
Wannan aikin na sa mummuna ne, zalunci ne mai girma, ta'addanci ne na zahiri.
Al'istigathaa fi fi'ilithalath, 1/32-33 Fasl fi bid'I'll awwal.

Shi'a a da kuwa, Tabrasiy malaminsu cewa ya yi:Aliy RA ya miqe don ya yi sallah ya zo masallaci ya yi sallah a bayan Abubakar.
Al'ihtijaj 1/94. Mir'aatul Uqul 5/340 Salim bn Qais p125
Tusiy ya ce wannan kar6a66e ne don zahiri ne, Talkhisus shafi p 354 na Tusiy.
To anya Aliy da iliminsa da imaninsa da riqo da addini zai yi salla a bayan mai sujjada wa gumaka? Qarya ne, dama qage suka yi wa sahabin Annabi Abubakr RA.

An rawaito daga Aliy RA yana cewa:
خير هذه الأمة بعد نبيها أبوبكر والثاني عمر
Mafificin wannan al'ummar bayan Annabinta Abubakar na Biyun Umar.
Manaqibul Imam Aliy,1/521 Babi na 53, na Muhammad Sulaiman Alkufiy malaminsu a qarni na 3, Muh'dul Mahmudiy ya yi tahqiqi, majma'u ihya'is saqafa na Iran suka buga 1412. Sai kuma Almuhraqa p 25 na Tustari.

Da aka tambaya Aliy akan mubaya'ar da ya yi wa Abubakar sai ya ce:
لولا أنا رأينا أبابكر لها أهلا لما تركناه
Ba don mun ga Abubakar ya cancanta ba, da ba mu bar shi ba.
Assaqifa wa fadak p40, na Abubakr Aljauhariy, tahaqiqin Muh'dl Aminiy.
Kenan sun tabbatar Aliy ya yi mubaya'a, amma don me 'yan shi'an yau suke nuna gaba tsakanin sabbannan da qirqiran qarya da kafurtawa, bayan Aliy RA bai yi haka ba, ya ma tabbatar da khalifancin Abubakar RA?

Like us on Facebook

No comments:

Post a Comment