Mai hankali ina son ka fahimci cewa larabawa asalinsu
a watse suke ba su san komai ba, ba wani cikakken
ilimin rayuwan duniya bare na lahira, ba su san tsarin
mulki na taruwa qarqashin mutun guda ba, bare a yi
maganar siyasa, zuwan Annabi ne duhu ya yaye,
wannan yana daya daga cikin mu'ujizar da Allah ya yi
wa muslunci, yadda ya turo manzo cikin irin wannan
al'ummar don duniya ta tabbatar cewa addinin daga
Allah ne, Allah SW yake cewa:
ﻣﺎ ﻛﻨﺖ ﺗﺘﻠﻮ ﻣﻦ ﻗﺒﻠﻪ ﻣﻦ ﻛﺘﺎﺏ ﻭﻻ ﺗﺨﻄﻪ ﺑﻴﻤﻴﻨﻚ ﺇﺫﺍ ﻻﺭﺗﺎﺏ
ﺍﻟﻤﺒﻄﻠﻮﻥ .
Ba ka riqa karanta wani littafi ba gabaninsa ko ka
rubata shi da hannunka bare ma6arnata su yi shakka.
Ankabuut.
To haka wannan al'umma ta taso, shi kuwa Abubakar
RA yana tare da Annabi ne tun suna yara a matsayin
abokai, ba su yi wani karatu ba, me yiwuwa wannan ne
dalilin da ya sa lamarin karatu da rubutun ya fadowa
Abubakar lokacin da aka kama fursunonin yaqi a Badar,
kenan sha'anin shugabanci da kwadayin mulki da fadi-
tashin siyasa ba sha'aninsu ba ne, Annabi shi ne
komai; shugaba, alqali, limami, amirul haj kuma
babban kwamandan bataliyar muslunci a wannan
zamanin, babu mai ikon matsawa sai abin da aka saka
shi.
To sai Annabi SAW ya dauki Abubakar suka tafi Madina
tare, ya nada shi Amirul haj, ya saka shi na'ibinsa a
sallah, wadannan sifofi ba bu mai su sai dai shi, don
haka shi ne a gaba har sai an za6i khalifa wanda zai
jagoranci jama'a, tunda Annabi bai nuna khalifa a
gwamnatance ba, rasuwar Annabi ba shakka ta razana
kowa, to amma shirya shi kamar wanka da sutura sai
waliyyansa wato ahlul baiti, da haka muslunci ya
tanada, in angama sai jama'a su zo a yi qoqarin sallah
da rufe shi.
A cikin wannan halin ne, aka sami labarin cewa Sa'ad
bn Ubadah yana wani taro na sirri a Saqifar Banu Sa'da
na janyo hankalin Madinawa kan a tsayar da khalifanci
ga 'yan Madina, a nan, wajibin Abubakar ne a matsayin
da Annabi ya dorashi wadan da muka fadi a baya, ya
tabbatar da haduwar kan musulmi, ya toshe kafar
fitinar da take qoqari ta kunnu tsakanin musulmai tun
ba a binne Annabi ba, don in aka bar lamarin ya girma
tabbas zai zama babbar fitina, Larabawa a wurin yaqi
qaramin abu yana iya haifar da yaqi na shekaru, bare
wannan da yake babba.
Alhamdu lillah, zuwansa ta yi amfani, ya kwantar da
hankula, wanda wajibinsa ne, sannan ya ba da dama a
fito da wanda ya cancanta ya jagoranci jama'a, ya fitar
da sunan wadan da yake ganin za su iya, su kuma suka
tabbatar da cewa, matuqar Annabi ya dora masa
nauyin wadancan abubuwa na baya, tabbas shi ne zai
jagoranci jama'a kuma a nan komai ya wuce, jama'a
suka fara yi masa mubaya'a daga wannan lokacin.
To da a ce lamarin ya yi girma kamar yadda wasu suke
fadi, ko a ce fin qarfi ne, ko son kai alhali jama'a ba sa
so, ko an sami rabuwar kai mai girma, ba shakka da an
rawaito irin ba-ta-kashin da aka yi a wurin, ko kashe-
kashe, ko jidali wanda zai dauki dogon lokaci ana
fafatawa, amma maganar a nan ta qare kowa ya watsar
aka yi mubaya'a, wannan kuwa dole ne, tun da Annabi
bai koyar da su yadda za su za6i khalifa a bayansa a
aika ce ba,bai kuma nuna wanda zai zama khalifan ba,
kenan dole a yi musu uziri a fitar da sugaban farko a
rayuwar muslunci bayan Annabi.
Mai hankali in baka manta ba, kwana Daya kafin rasuwar Annabi SAW ya raba dukiyar da ke hannunsa ta kudi, ya kuma 'yanta bayinsa ya kyautar da makaminsa don daukaka kalmar Allah, wannan tabbatar da hadisi mashahuri wanda sahabbai mafi yawa suka rawaito ciki har da Aliy RA. Ba kamar yadda shi'a suke cewa Abubakar ne kawai ya rawaito ba,wanda yake cewa Fatimah RA ta zo wurin Abubakar RA neman gadonta,wanda Annabi ya bari na Fadak da sauransu, sai Abubakar RA ya ce: Na ji Annabi SAW yana cewa:
إنا لا نورث ماتركناه صدقة. البخاري
Mu ba a gadonmu abin da muka bari sadaqa ne.
Tun daga wannan ranar Fatima RA ba ta sake yi masa magana ba, koda yake 'yan Shi'a sun fassara wannan da cewa ba ta sake magana da shi ba, sabo da fushi da shi da take yi, alhali ba ta sake yi masa maganar gadon ba ne, uzirin da za a yi a nan shi ne, ta tambaye shi ne don ba ta sani ba,amma tun da aka gaya mata kuma shikenan, ba ta sake komawa ga maganar ba.
Abubakar RA ya ci gaba da ba Ahlul baiti ciki har da 'yarsa A'ishah haqqoqinsu na fai'in Madina da Khumusin Khaibar da Fadak, amma bai ba da gado ba, kamar yadda Annabi SAW ya raba kayansa na gida don kada ya bar gadon.
Amma abin da ake rawaitowa daga shi'a shi ne, Abubakar da Umar RA, sun qwace filin Fadak din sun hana Fatimah RA gadonta, shi Fadak wani qauye ne a lokacin kusa da Madina, na Yahudawa, aka yi sulhu da su suka fita suka barwa Annabi SAW a matsayin na sa shi kadai, to in kana karatun rubuce-rubucensu sai ka ga wani lokaci suna cewa gadonta ne aka hana, in suka ga A'ishah 'yar Abubakar RA, da Hafsah 'yar Umar RA suna ciki kuma hankali ba zai dauki cewa Fatimah ta je nemo hakkinsu ne, ba na ta ba a wurin kuma iyayensu, sai su ce a'a ba gado ba ne dama kyauta ya ba ta kafin ya rasu, don sabo da kudin da take samu a wurin tana taimakon talakawa, ta yi baqin ciki da su har wannan ya kashe ta! Kar mu manta, Abubakar da Umar, Usman da Aliy RA ba wanda ya yi qoqarin ba iyalan Annabi gado don ya san wancan hadisin, in kuma da hakkin Fatimah RA ne da Aliy RA da ya hau khalifa ya kar6o mata, kenan zargin ciki har da shi.
Mai hankali! Abin da ake cewa shi ne, Umar RA ya daki Fatimah, ya karya mata kashin qirji, ya zubar mata da ciki, ya hada ta da qofa, da sauran abubuwa munana da suka fada, amma mun sani wata Shida ne kacal bayan rasuwar Annabi Fatimah RA ta bi shi, to yaushe ta warke qashin qirjin har da ta je neman gado? Ashe asarar jaririnta bai fi gado girma ba, ya aka yi bata rasu da baqin cikin kashe mata jariri ba sai qasar da aka kar6a daga hannun Yahudawa? Ba sun ce wai Umar RA ya dake ta ya hada ta da qofa ba, duk wannan bai ba ta haushi ba ya sa ta rasa ranta, sai gado? Shin ina khalifancin da aka kar6a a wurin ahlul baiti, wanda shisshike ne daga cikin shika-shikan muslunci a wurin 'yan shi'a, me ya sa ba ta rasu da baqin cikin an kar6e ba sai gado? Wai ina jarumtakar da shi'a kullum suke fadi na Aliy RA shin Fatimah RA koda ba matarsa ba ce shin ita ba ahlul baiti ba ce, ko ya yarda da abin da aka ce sun yi ne? Me ya sa ba mu ji yaqin da ya yi da kowa ba daga cikinsu? To shi'a kenan malam, Allah ya qara shiryar da mu.
Like us on Facebook
No comments:
Post a Comment