MARASA AURE( MAZA da MATA )Wa iyazu billah
MU BUDE KUNNE MUJI
akwai wani bala'i wanda ya kunno ma
al'ummar musulmi kai... Ita
wannan musibah ta fi aukuwa ne ga marasa
aure...
Zaka iske namiji ko mace a duk
sa'ar da sha'awarsu ta motsa sai
su rika wasa da al'aurar su har
sha'awar tasu ta kwanta (fitar da
maniyyi) wannan shi ake kira da suna Istimna'i
ko masterbation a
turance.....
Ganin haka yasa nayi
farautar
fatawa daga
wasu malamai a kan ko mene ne
hukuncin abun a musulunci
sai malam ya ce
''Duk mai yin
ISTIMNA
(MASTURBATION) Mace ko
Namiji, idan har bai tuba ya daina
ba, ko idan har bata tuba ta daina
ba, babu mamaki daya daga cikin cututtukan
nan guda goma (10) ya same ta/
SHI, ko
kuma
ma sama da ciwo daya ya sameta,
ko ya sameshi. ALLAH YA KAREMU,
AMIN.
1-Yana Rage karfin ido
2-Rage karfin namiji ko mace a
wajen kwanciya, kanaso ka biya
bukata amma ba dama.
3-Yana shafar lafiyar jijiyoyin da
suke da ala’ka da fitar maniyyi, ko
yasa duk
lokacin da zakayi fitsari sai kaji
kamar ana tsira allura a cikin gabanka (zafi
sosai)
4- Yana
haifar da wani irin ciwo a
cikin mutum
5- Yana shafar lafiyar ‘ya’yan maraina, kuma
ya kankantar da
gaban namiji
ya koma kamar na karamin yaro.
6- Yana sa
saurin fitar
maniyyi a lokacin saduwa
7- Yana kawo ciwon
kashin
gadonbaya
8- Yana rage kaurin maniyyi,
wanda kuma zai iya shafar lafiyar
abin da za a haifa, koma ya hana
haihuwar gabadaya
9-Yana sa kuraje a jikin
mutum
10-Yana rage kaifin
kwakwalwa
MAI NEMAN KARIN BAYANI YA DUBA CIKIN
LITTAFIN FATAWA
NA
SHEKH BN BAZ DA SHEKH
UTHAIMIN
DA KUMA SHEKH BN JUBAIRU,
JUZ’I NA BIYU SHAFI NA 132-133''
Bayan malam ya kare fatawar sa
sai muka tuntubi wani mai kula
da Lafiya shima ya ce; ''kasan
maniyyin da ke fita kadan ne,
sabili da ba a ainihin saduwa ne maniyyin ya
fita ba, so saura zai
rage kuma zai yi ta taruwa a
mararsa da haka sai ya ja masa
illoli ta fuskar Lafiyar sa. Misali duk
mai yin wannan abuzaka iske
yana shan wahala ko yaya ne wajen fitsari.
To ina anfanin
wannan'' To yan'uwana sai mu
dage mu yi aure ko mu yawaita
azumin nafila da karatun alqur'ani
da kasancewa da muminan
abokai da gujewa fasikan abokanai....
Sannan mu ji tsoron
Allah mu guji kallace kallacen
banza da wofi.
Allah ya kara kare wadanda basu
aikata
wannan mummunan bala'in su kuwa
wadanda keyi Allah (s.w.t) ya
shirye su su
daina.
No comments:
Post a Comment