Mai hankali ina so ka fahimci cewa duk Annabawan da suka rayu tun zamanin Annabi Ibrahim ba su gangaro inda Larabawa suke ba, suna can Yamma ne daga Masar zuwa Palastine. Zuwa Iraq, sai dai da yake Annabi Ibrahim ya kai Hajir da danta Annabi Isma'il Makka, inda wasu Larabawa suka zo wurin, har Annabi Isma'eel ya yi aure a cikinsu shi ma ya rikide ya zama Balarabe, 'ya'yansa suka fito Larabawa, wurin ya zama gari wanda Larabawa suke zaune, kimanin shekara dubu Hudu kenan, Ba shakka sun tafi a kan addinin Annabi Ibrahim ne wanda Isma'eel AS ya tashi da shi a cikinsu, kuma ba wani sabon Annabi da ya zo musu, sai lokacin zuwan Annabi SAW da ya biyo tsatson Isma'il din dan Ibrahim AS.
A kimance akwai shekara dubu Biyu kenan suna zaune ba wani Annabi, a duk tsawon wannan lokacin, sa6anin Banu Isra'ila da suka sami Manzanni 16, Daya bayan Daya, duk da haka Larabawa sun yi qoqarin riqe addinin Annabi Ibrahim har kusan turo Annabi SAW, inda daga baya suka canja kamar yadda muka fadi a baya.
Wannan yanki na su cike yake da hargitsi, babu saqon annabci, ba ci gaba na ilimi, ba lafiyayyar qasa ta noma, ba wani abu na ci gaba, don haka ko 'yan kasuwansu sai dai su je qasashen waje wurin kasuwancinsu, shi ya sa ko qasashen duniya ba su yi kwadayin mamayar yankin ba.
Qasashen duniya masu qarfin yaqi a lokacin daular Rumawa ce da take hadiye birane, sai Farisawa wato Iraniyawa, sun yi ta samun yaqoqi ko a tsakaninsu, a lokacin da Rumawa suka so yaqin Larabawa ba su sha wata wahala ba, don Larabawan kansu a rabe ne, ga shi yaqi a tsakanunsu ya fatattaka su, haka suka zauna qarqashin Rumawa har sai da Iraniyawa suka hada hannu da Larabawan suka kori Rumawa, to amma su ma sai suka mamaye Larabawan, sai lokacin da Habashawa suka hada hannu da Larabawan suka yaqi Iraniyawa, to amma su ma suka mamaye su, shekarar haihuwar Annabi SAW ita ce lokacin farko da Larabawa suka ta6a yaqar wata daula suka ci nasara, wannan rarrabuwa dake tsakaninsu da rashin wayewa na rayuwa ko rashin sanin dabarun yaqi ya ci gaba har sai da Allah ya aiko Annabinsa SAW, don nuna mu'ujizancin manzon a inda aka samo shi.
Ba wani abu da ya zama musu darasi, kullum cikin gaba suke da musluncin, don an sami tsawon lokaci ba wani manzo, daga cikinsu akwai Umar bnl Khattab, matashi ne dan shekara Talatin da wani abu, yana da zafi ga haiba, kowa yana tsoronsa a wannan yankin, don Allah ya ba shi hazaqa da jarumtaka ga hangen nesa, ta kai ga yana iya fuskantar duk wata fitina ba tare da wani tsoro ba kuma ya yi maganinta, to amma ga muslunci yana yi wa yankinsa da addinin iyayensa barazana.
SHIN WAYE UMAR (RA)??????????
Umar bnl Khattab RA ba wanda zai sifanta maka shi sai ya gaya maka wasu dabi'u guda Biyu, ya ce maka mai kaushi ne kuma mai zafin zuciya, to amma abin mamaki, in dai lamarin yana da alaqa da muslunci za ka taras ya fi ruwa laushi, domin kuwa lokacin da ya zaro takobi ya nufi Annabi shi kadai a cikin sahabbansa, ko a mutu ko a yi rai, sai aka gaya masa cewa qanwarsa fa Fatima bintul Khattab ita da mijinta Sa'eed bn Zaid sun muslunta, take ya ti kwana ya sami Sa'eed ya dake shi. ita ma ya wanke ta da mari, ya nemi ta ba shi yankin Qur'anin da take karantawa, ta ce shi najasa ne sai ya yi tsarki, haka dole ya yi ba tare da ya buge ta ya qwace ba, kuma sanadiyyar musluntarsa kenan.
Shigar Umar RA muslunci duk sauran da suka riga shi suka sami 'yancin yin ibada, abin da ya fi ingantuwa shi ne bai muslunta ba sai bayan hijira zuwa Habasha, a iya cewa bayan muslunci da shekara 13, don muslunci ya zo ne a 0610AD, a lokacin yana da shekara 32, ka iya cewa Annabi ya girme shi da shekara 13, amma adadin musulmai gaba daya 39 ne, shi ne cikon na 40, wasu suna son muslunci amma suna tsoron rayukansu, musluntarsa ta canja rayuwar muslunci gaba daya; (a)Ta ba muslmai 'yancin nuna addininsu da cewa su musulmai ne. (b)Ta ba masu kwadayin addinin damar shigowa ba tare da tsoro ba.
Umar ya ba da shawarar yin dawafi ba tare da fargaba ba, ya kuma shiga gaba ya yi jagorancin sahun farko Annabi SAW yana na tsakiya, Hamza bn Abdil Muttalib ya yi jagorancin Daya sahun, a lokacin da hijira zuwa madina ta kama, Umar RA ya fita tare da sauran sahabbai don cika umurnin Annabi SAW.
Umar RA ya halarci yaqin Badar, Uhud, Khandaq, Nadeer, Khaibar, Hunain, Ta'if da kuma Tabuka, tarihi ya dauko mas'alar Sulhu Hudaibiyya da Umar RA da Fat'hu Makka, shi ne mutum na farko da ya ba Annabi SAW amsa game da yaqin mushrikai a Badar bayan Abubakar RA, duk da hamiyya ta Larabawa amma shi ne ya kashe kawunsa Aas bn Hisham a wannan yaqin, shi ne ya yi wa Abu Sufyan raddi a yaqin Uhudu lokacin da yake tambaya ko Annabi yana da rai, an tabbatar da cewa ya ba da rabin dukiyarsa a babban shirin yaqi na qarshe a rayuwar Annabi SAW wato Tabuka.
A duk wannan zafi na Umar RA da ake fadi da zarar ka ce Allah SW ya ce kaza ko Annabi SAW ya ce kaza to shi kenan, nan take za ka tsai da shi, Umar RA bai ta6a tsallake maganar Allah SW ba ko ta Annabi SAW, za mu gani qarara, yadda Annabi SAW ya auri 'yarsa Hafsah, wannan yana tabbatar da tsarkin Umar RA a muslunce, domin Annabi ya hana Aliy RA ya auri 'yar Abu Jahal don 'yar Annabci ba za ta yi kishiya da 'yar kafurci ba, to bare kuma a ce Annabin ne zai auri 'yar kafurci haram! Haka Annabi SAW ya rasu yana mai amincewa da Umar RA.
Like us on Facebook