Tuesday, 24 December 2013

MAI HANKALI YI TUNANI! 6.

By: Baban Manar Alkhasim

Mai hankali ina so ka fahimci cewa duk Annabawan da suka rayu tun zamanin Annabi Ibrahim ba su gangaro inda Larabawa suke ba, suna can Yamma ne daga Masar zuwa Palastine. Zuwa Iraq, sai dai da yake Annabi Ibrahim ya kai Hajir da danta Annabi Isma'il Makka, inda wasu Larabawa suka zo wurin, har Annabi Isma'eel ya yi aure a cikinsu shi ma ya rikide ya zama Balarabe, 'ya'yansa suka fito Larabawa, wurin ya zama gari wanda Larabawa suke zaune, kimanin shekara dubu Hudu kenan, Ba shakka sun tafi a kan addinin Annabi Ibrahim ne wanda Isma'eel AS ya tashi da shi a cikinsu, kuma ba wani sabon Annabi da ya zo musu, sai lokacin zuwan Annabi SAW da ya biyo tsatson Isma'il din dan Ibrahim AS.

A kimance akwai shekara dubu Biyu kenan suna zaune ba wani Annabi, a duk tsawon wannan lokacin, sa6anin Banu Isra'ila da suka sami Manzanni 16, Daya bayan Daya, duk da haka Larabawa sun yi qoqarin riqe addinin Annabi Ibrahim har kusan turo Annabi SAW, inda daga baya suka canja kamar yadda muka fadi a baya.

Wannan yanki na su cike yake da hargitsi, babu saqon annabci, ba ci gaba na ilimi, ba lafiyayyar qasa ta noma, ba wani abu na ci gaba, don haka ko 'yan kasuwansu sai dai su je qasashen waje wurin kasuwancinsu, shi ya sa ko qasashen duniya ba su yi kwadayin mamayar yankin ba.

Qasashen duniya masu qarfin yaqi a lokacin daular Rumawa ce da take hadiye birane, sai Farisawa wato Iraniyawa, sun yi ta samun yaqoqi ko a tsakaninsu, a lokacin da Rumawa suka so yaqin Larabawa ba su sha wata wahala ba, don Larabawan kansu a rabe ne, ga shi yaqi a tsakanunsu ya fatattaka su, haka suka zauna qarqashin Rumawa har sai da Iraniyawa suka hada hannu da Larabawan suka kori Rumawa, to amma su ma sai suka mamaye Larabawan, sai lokacin da Habashawa suka hada hannu da Larabawan suka yaqi Iraniyawa, to amma su ma suka mamaye su, shekarar haihuwar Annabi SAW ita ce lokacin farko da Larabawa suka ta6a yaqar wata daula suka ci nasara, wannan rarrabuwa dake tsakaninsu da rashin wayewa na rayuwa ko rashin sanin dabarun yaqi ya ci gaba har sai da Allah ya aiko Annabinsa SAW, don nuna mu'ujizancin manzon a inda aka samo shi.

Ba wani abu da ya zama musu darasi, kullum cikin gaba suke da musluncin, don an sami tsawon lokaci ba wani manzo, daga cikinsu akwai Umar bnl Khattab, matashi ne dan shekara Talatin da wani abu, yana da zafi ga haiba, kowa yana tsoronsa a wannan yankin, don Allah ya ba shi hazaqa da jarumtaka ga hangen nesa, ta kai ga yana iya fuskantar duk wata fitina ba tare da wani tsoro ba kuma ya yi maganinta, to amma ga muslunci yana yi wa yankinsa da addinin iyayensa barazana.

SHIN WAYE UMAR (RA)??????????

Umar bnl Khattab RA ba wanda zai sifanta maka shi sai ya gaya maka wasu dabi'u guda Biyu, ya ce maka mai kaushi ne kuma mai zafin zuciya, to amma abin mamaki, in dai lamarin yana da alaqa da muslunci za ka taras ya fi ruwa laushi, domin kuwa lokacin da ya zaro takobi ya nufi Annabi shi kadai a cikin sahabbansa, ko a mutu ko a yi rai, sai aka gaya masa cewa qanwarsa fa Fatima bintul Khattab ita da mijinta Sa'eed bn Zaid sun muslunta, take ya ti kwana ya sami Sa'eed ya dake shi. ita ma ya wanke ta da mari, ya nemi ta ba shi yankin Qur'anin da take karantawa, ta ce shi najasa ne sai ya yi tsarki, haka dole ya yi ba tare da ya buge ta ya qwace ba, kuma sanadiyyar musluntarsa kenan.

Shigar Umar RA muslunci duk sauran da suka riga shi suka sami 'yancin yin ibada, abin da ya fi ingantuwa shi ne bai muslunta ba sai bayan hijira zuwa Habasha, a iya cewa bayan muslunci da shekara 13, don muslunci ya zo ne a 0610AD, a lokacin yana da shekara 32, ka iya cewa Annabi ya girme shi da shekara 13, amma adadin musulmai gaba daya 39 ne, shi ne cikon na 40, wasu suna son muslunci amma suna tsoron rayukansu, musluntarsa ta canja rayuwar muslunci gaba daya; (a)Ta ba muslmai 'yancin nuna addininsu da cewa su musulmai ne. (b)Ta ba masu kwadayin addinin damar shigowa ba tare da tsoro ba.

Umar ya ba da shawarar yin dawafi ba tare da fargaba ba, ya kuma shiga gaba ya yi jagorancin sahun farko Annabi SAW yana na tsakiya, Hamza bn Abdil Muttalib ya yi jagorancin Daya sahun, a lokacin da hijira zuwa madina ta kama, Umar RA ya fita tare da sauran sahabbai don cika umurnin Annabi SAW.

Umar RA ya halarci yaqin Badar, Uhud, Khandaq, Nadeer, Khaibar, Hunain, Ta'if da kuma Tabuka, tarihi ya dauko mas'alar Sulhu Hudaibiyya da Umar RA da Fat'hu Makka, shi ne mutum na farko da ya ba Annabi SAW amsa game da yaqin mushrikai a Badar bayan Abubakar RA, duk da hamiyya ta Larabawa amma shi ne ya kashe kawunsa Aas bn Hisham a wannan yaqin, shi ne ya yi wa Abu Sufyan raddi a yaqin Uhudu lokacin da yake tambaya ko Annabi yana da rai, an tabbatar da cewa ya ba da rabin dukiyarsa a babban shirin yaqi na qarshe a rayuwar Annabi SAW wato Tabuka.

A duk wannan zafi na Umar RA da ake fadi da zarar ka ce Allah SW ya ce kaza ko Annabi SAW ya ce kaza to shi kenan, nan take za ka tsai da shi, Umar RA bai ta6a tsallake maganar Allah SW ba ko ta Annabi SAW, za mu gani qarara, yadda Annabi SAW ya auri 'yarsa Hafsah, wannan yana tabbatar da tsarkin Umar RA a muslunce, domin Annabi ya hana Aliy RA ya auri 'yar Abu Jahal don 'yar Annabci ba za ta yi kishiya da 'yar kafurci ba, to bare kuma a ce Annabin ne zai auri 'yar kafurci haram! Haka Annabi SAW ya rasu yana mai amincewa da Umar RA.

Like us on Facebook

Saturday, 21 December 2013

What does "Islam" mean?:

Via: Islam in Nigeria

The word "Islam" itself means "Submission to Allah." The religion of Islam is not named after a person as in the case of "Christianity" which was named after Jesus Christ, "Buddhism" after Gotama Buddha, "Marxism" after Karl Marx, and "Confucianism" after Confucius. Similarly, Islam is not named after a tribe like "Judaism" after the tribe of Judah and "Hinduism" after the Hindus. The Arabic word "Islam" means the submission or surrender of one's will to the will of the only true god worthy of worship, "Allah" (known as God "the Father" in Christianity). Anyone who does indeed submit to the will of Allah as required by Islam is termed a "Muslim," which means one who has submitted to the will of Allah. Many people in the West have developed the sad misinformed trend of calling Islam "Muhammadenism" and it's followers "Muhammadins." This is a totally foreign word to Muslims and unrecognized by them. No Muslim has ever called his religion "Muhammadenism" or called himself a "Muhammadin."

Thursday, 19 December 2013

MAI HANKALI YI TUNANI! 5

By:  Baban Manar Alkhasim

Mai hankali, saninka ne cewa dukiyar Abubakar ce ta farkon da aka fara aiki da ita wurin daukaka kalmar Allah bayan ta Khadijah RA, sannan saninka ka ne cewa ya rasu a talakansa ne ba kamar yadda ya shiga muslunci ba, sa6anin shugaban 'yan gwagwarmayan Nigeria, da ya shiga a talakansa yanzu yana hawa manyan motoci ga makadeden gida ga maqudan kudi a banki.

Bayan rasuwar Annabi SAW Abubakar RA ya ci gaba da jagorancin musulmai da bude qasashe ana yada muslunci, wanda wannan ne Annabi SAW yake yi, ba wani abu da Abubakar ya qara ko ya rage, kamar dai yadda ya fadi a hudubarsa cewa a yi masa biyayya matuqar ya bi umurnin Allah, sannan a sa6a masa matuqar ya sa6a wa umurnin Allah, Abubakar ya ba da 'yancin a yi fito na fito da shi matuqar ba shi a kan daidai, kenan shurun da Aliy RA ya yi, da rashin fuskantar Abubakar RA game da sha'anin khalifanci yana nuna gamsuwarsa da lamarin.

Zancen 'yan ridda da Abubakar RA ya yaqa ba kashi Daya ba ne, 'yan shi'a suna qoqarin nuna cewa Abubakar RA ya yaqi wadan da suka sa6a masa ne a siyasarsa alhali wannan qage ne na masamman, akwai qabilu da suka yi ridda kowanne da dalilinsa: Banu Asad da Gatfan, Banu Kinda, Banu Mazhaj, Banu Hanifa, Banu Sulaim, Banu Tameem.

Sabbin shiga muslunci wadan da imani bai gama ratsa zukatansu ba, ba shakka dukiyarsu ta fi musu musluncin, shi ya sa Annabi na rasuwa suka ce ba za su ba da zakka ba, wace rukuni ce daga cikin rukunnan muslunci, Abubakar ya nemi su juyo zuwa ga addini ko a saka su dole, suka za6i yaqi, aka yaqe su, aka musluntar da su dole, akwai Al'Aswadul Unsiy ya yi ridda tun Annabi bai bar duniya ba ya koma Yemen tare da sojojinsa su 700, Abubakar ya yake su.

Akwai wadan da suka yi da'awar Annabci, ciki harda Aswad din da Musailama da Sujahut Tamimiyya,duk wadannan Abubakar RA ya yaqe su ya dawo da kalma ta zamo guda Daya, sannan akwai mutanen Baharain da suka ce tun da fa Annabi SAW ya rasu to ba su ba muslunci domin da shi Annabi ne da bai rasu ba, wadannan sun yi ridda gaba dayansu in ba wani qauye da ake kira Juwaathaa'u ba, haka Abubakar ya yaqe su ya sa suka dawo muslunci.

Abubakar RA bai fara yada muslunci ba sai da ya tabbatar kan Al'umma ya dawo ya sake dinkewa kamar yadda Annabi SAW ya bar shi, daga nan ya fara bude qasashen da shi'a suke a yau, ba shakka har Annabi ya rasu suna kafurcinsu ne, ba su san muslunci ba sai Khalifancin Abubakar wanda yau suke cewa kafuri ne bayan ya musluntar da su, ya bude Iraqi da qasashen Sham Allah ya qara yadda a gare shi.

Mai hankali ina so yau mu duba wasu lamarori ne masu mahimmanci ni da kai, ka san dai mun gabatar da rayuwar Abubakar RA yadda ya yi ta da Annabi SAW, da abin da muka fitar a ciki na ilimi wanda hankalinka zai tabbatar maka da yadda rayuwar take, to ya matsayin Abubakar a wurin 'yan shi'an yanzu?

Shi'an yanzu suka ce: Abubakar ya qi fadin kalmar shahada lokacin rasuwarsa, ya bayyana da kansa cewa zai shiga (Wani akwati na wuta, wanda aka kulle yake da kwadon wuta, a ciki akwai mutum 12 da ni da wannan abokin nawa, na ce Umar ya ce: Qwarai, da kuma wawukeken rami na Jahannama da wani dutse a samansa idan Ubangiji yana son ya hura wutar sai ya daga dutsen.
Sulaim bin Qais p208 Ba'du aqwali Muhammad bn Abibakr Bugun Darul irshad. Bihaar 30/131 Babu ma azhara Abubakr wa Umar.

Asafwil Jaza'iriy yace:
إن أبابكر كان يصلي خلف رسول الله ص والصنم معلق في عنقه وسجوده عليه.
Haqiqa Abubakr ya riqa salla a bayan Annabi SAW alhali akwai gunki a rataye da wuyarsa, a kansa yake sujjada.
Al'anwarul Nu'maniyya 1/53. Nur Murtadwiy,
Hatta yaqin 'yan ridda da ya yi sai da suka ce
فكان هذا الفعل منه فعلا فظيعا، وظلما عظيما، وتعديا بينا.
Wannan aikin na sa mummuna ne, zalunci ne mai girma, ta'addanci ne na zahiri.
Al'istigathaa fi fi'ilithalath, 1/32-33 Fasl fi bid'I'll awwal.

Shi'a a da kuwa, Tabrasiy malaminsu cewa ya yi:Aliy RA ya miqe don ya yi sallah ya zo masallaci ya yi sallah a bayan Abubakar.
Al'ihtijaj 1/94. Mir'aatul Uqul 5/340 Salim bn Qais p125
Tusiy ya ce wannan kar6a66e ne don zahiri ne, Talkhisus shafi p 354 na Tusiy.
To anya Aliy da iliminsa da imaninsa da riqo da addini zai yi salla a bayan mai sujjada wa gumaka? Qarya ne, dama qage suka yi wa sahabin Annabi Abubakr RA.

An rawaito daga Aliy RA yana cewa:
خير هذه الأمة بعد نبيها أبوبكر والثاني عمر
Mafificin wannan al'ummar bayan Annabinta Abubakar na Biyun Umar.
Manaqibul Imam Aliy,1/521 Babi na 53, na Muhammad Sulaiman Alkufiy malaminsu a qarni na 3, Muh'dul Mahmudiy ya yi tahqiqi, majma'u ihya'is saqafa na Iran suka buga 1412. Sai kuma Almuhraqa p 25 na Tustari.

Da aka tambaya Aliy akan mubaya'ar da ya yi wa Abubakar sai ya ce:
لولا أنا رأينا أبابكر لها أهلا لما تركناه
Ba don mun ga Abubakar ya cancanta ba, da ba mu bar shi ba.
Assaqifa wa fadak p40, na Abubakr Aljauhariy, tahaqiqin Muh'dl Aminiy.
Kenan sun tabbatar Aliy ya yi mubaya'a, amma don me 'yan shi'an yau suke nuna gaba tsakanin sabbannan da qirqiran qarya da kafurtawa, bayan Aliy RA bai yi haka ba, ya ma tabbatar da khalifancin Abubakar RA?

Like us on Facebook

MAI HANKALI YI TUNANI! 4

By: Baban Manar Alkasim

Mai hankali ina son ka fahimci cewa larabawa asalinsu
a watse suke ba su san komai ba, ba wani cikakken
ilimin rayuwan duniya bare na lahira, ba su san tsarin
mulki na taruwa qarqashin mutun guda ba, bare a yi
maganar siyasa, zuwan Annabi ne duhu ya yaye,
wannan yana daya daga cikin mu'ujizar da Allah ya yi
wa muslunci, yadda ya turo manzo cikin irin wannan
al'ummar don duniya ta tabbatar cewa addinin daga
Allah ne, Allah SW yake cewa:
ﻣﺎ ﻛﻨﺖ ﺗﺘﻠﻮ ﻣﻦ ﻗﺒﻠﻪ ﻣﻦ ﻛﺘﺎﺏ ﻭﻻ ﺗﺨﻄﻪ ﺑﻴﻤﻴﻨﻚ ﺇﺫﺍ ﻻﺭﺗﺎﺏ
ﺍﻟﻤﺒﻄﻠﻮﻥ .
Ba ka riqa karanta wani littafi ba gabaninsa ko ka
rubata shi da hannunka bare ma6arnata su yi shakka.
Ankabuut.

To haka wannan al'umma ta taso, shi kuwa Abubakar
RA yana tare da Annabi ne tun suna yara a matsayin
abokai, ba su yi wani karatu ba, me yiwuwa wannan ne
dalilin da ya sa lamarin karatu da rubutun ya fadowa
Abubakar lokacin da aka kama fursunonin yaqi a Badar,
kenan sha'anin shugabanci da kwadayin mulki da fadi-
tashin siyasa ba sha'aninsu ba ne, Annabi shi ne
komai; shugaba, alqali, limami, amirul haj kuma
babban kwamandan bataliyar muslunci a wannan
zamanin, babu mai ikon matsawa sai abin da aka saka
shi.

To sai Annabi SAW ya dauki Abubakar suka tafi Madina
tare, ya nada shi Amirul haj, ya saka shi na'ibinsa a
sallah, wadannan sifofi ba bu mai su sai dai shi, don
haka shi ne a gaba har sai an za6i khalifa wanda zai
jagoranci jama'a, tunda Annabi bai nuna khalifa a
gwamnatance ba, rasuwar Annabi ba shakka ta razana
kowa, to amma shirya shi kamar wanka da sutura sai
waliyyansa wato ahlul baiti,  da haka muslunci ya
tanada, in angama sai jama'a su zo a yi qoqarin sallah
da rufe shi.

A cikin wannan halin ne, aka sami labarin cewa Sa'ad
bn Ubadah yana wani taro na sirri a Saqifar Banu Sa'da
na janyo hankalin Madinawa kan a tsayar da khalifanci
ga 'yan Madina, a nan, wajibin Abubakar ne a matsayin
da Annabi ya dorashi wadan da muka fadi a baya, ya
tabbatar da haduwar kan musulmi, ya toshe kafar
fitinar da take qoqari ta kunnu tsakanin musulmai tun
ba a binne Annabi ba, don in aka bar lamarin ya girma
tabbas zai zama babbar fitina, Larabawa a wurin yaqi
qaramin abu yana iya haifar da yaqi na shekaru, bare
wannan da yake babba.

Alhamdu lillah, zuwansa ta yi amfani, ya kwantar da
hankula, wanda wajibinsa ne, sannan ya ba da dama a
fito da wanda ya cancanta ya jagoranci jama'a, ya fitar
da sunan wadan da yake ganin za su iya, su kuma suka
tabbatar da cewa, matuqar Annabi ya dora masa
nauyin wadancan abubuwa na baya, tabbas shi ne zai
jagoranci jama'a kuma a nan komai ya wuce, jama'a
suka fara yi masa mubaya'a daga wannan lokacin.
To da a ce lamarin ya yi girma kamar yadda wasu suke
fadi, ko a ce fin qarfi ne, ko son kai alhali jama'a ba sa
so, ko an sami rabuwar kai mai girma, ba shakka da an
rawaito irin ba-ta-kashin da aka yi a wurin, ko kashe-
kashe, ko jidali wanda zai dauki dogon lokaci ana
fafatawa, amma maganar a nan ta qare kowa ya watsar
aka yi mubaya'a, wannan kuwa dole ne, tun da Annabi
bai koyar da su yadda za su za6i khalifa a bayansa a
aika ce ba,bai kuma nuna wanda zai zama khalifan ba,
kenan dole a yi musu uziri a fitar da sugaban farko a
rayuwar muslunci bayan Annabi.

Mai hankali in baka manta ba, kwana Daya kafin rasuwar Annabi SAW ya raba dukiyar da ke hannunsa ta kudi, ya kuma 'yanta bayinsa ya kyautar da makaminsa don daukaka kalmar Allah, wannan  tabbatar da hadisi mashahuri wanda sahabbai mafi yawa suka rawaito ciki har da Aliy RA. Ba kamar yadda shi'a suke cewa Abubakar ne kawai ya rawaito ba,wanda yake cewa Fatimah RA ta zo wurin Abubakar RA neman gadonta,wanda Annabi ya bari na Fadak da sauransu, sai Abubakar RA ya ce: Na ji Annabi SAW yana cewa:
إنا لا نورث ماتركناه صدقة. البخاري
Mu ba a gadonmu abin da muka bari sadaqa ne.

Tun daga wannan ranar Fatima RA ba ta sake yi masa magana ba, koda yake 'yan Shi'a sun fassara wannan da cewa ba ta sake magana da shi ba, sabo da fushi da shi da take yi, alhali ba ta sake yi masa maganar gadon ba ne, uzirin da za a yi a nan shi ne, ta tambaye shi ne don ba ta sani ba,amma tun da aka gaya mata kuma shikenan, ba ta sake komawa ga maganar ba.

Abubakar RA ya ci gaba da ba Ahlul baiti ciki har da 'yarsa A'ishah haqqoqinsu na fai'in Madina da Khumusin Khaibar da Fadak, amma bai ba da gado ba, kamar yadda Annabi SAW ya raba kayansa na gida don kada ya bar gadon.

Amma abin da ake rawaitowa daga shi'a shi ne, Abubakar da Umar RA, sun qwace filin Fadak din sun hana Fatimah RA gadonta, shi Fadak wani qauye ne a lokacin kusa da Madina, na Yahudawa, aka yi sulhu da su suka fita suka barwa Annabi SAW a matsayin na sa shi kadai, to in kana karatun rubuce-rubucensu sai ka ga wani lokaci suna cewa gadonta ne aka hana, in suka ga A'ishah 'yar Abubakar RA, da Hafsah 'yar Umar RA suna ciki kuma hankali ba zai dauki cewa Fatimah ta je nemo hakkinsu ne, ba na ta ba a wurin kuma iyayensu, sai su ce a'a ba gado ba ne dama kyauta ya ba ta kafin ya rasu, don sabo da kudin da take samu a wurin tana taimakon talakawa, ta yi baqin ciki da su har wannan ya kashe ta! Kar mu manta, Abubakar da Umar, Usman da Aliy RA ba wanda ya yi qoqarin ba iyalan Annabi gado don ya san wancan hadisin, in kuma da hakkin Fatimah RA ne da Aliy RA da ya hau khalifa ya kar6o mata, kenan zargin ciki har da shi.

Mai hankali! Abin da ake cewa shi ne, Umar RA ya daki Fatimah, ya karya mata kashin qirji, ya zubar mata da ciki, ya hada ta da qofa, da sauran abubuwa munana da suka fada, amma mun sani wata Shida ne kacal bayan rasuwar Annabi Fatimah RA ta bi shi, to yaushe ta warke qashin qirjin har da ta je neman gado? Ashe asarar jaririnta bai fi gado girma ba, ya aka yi bata rasu da baqin cikin kashe mata jariri ba sai qasar da aka kar6a daga hannun Yahudawa? Ba sun ce wai Umar RA ya dake ta ya hada ta da qofa ba, duk wannan bai ba ta haushi ba ya sa ta rasa ranta, sai gado? Shin ina khalifancin da aka kar6a a wurin ahlul baiti, wanda shisshike ne daga cikin shika-shikan muslunci a wurin 'yan shi'a, me ya sa ba ta rasu da baqin cikin an kar6e ba sai gado? Wai ina jarumtakar da shi'a kullum suke fadi na Aliy RA shin Fatimah RA koda ba matarsa ba ce shin ita ba ahlul baiti ba ce, ko ya yarda da abin da aka ce sun yi ne? Me ya sa ba mu ji yaqin da ya yi da kowa ba daga cikinsu? To shi'a kenan malam, Allah ya qara shiryar da mu.

Like us on Facebook

Wednesday, 4 December 2013

NASIHAR MARIGAYI SHEIKH JA'AFAR KANO ANA I GOBE ZA'A HARBE SHI, AKAN SIYASA

Wannan Nasihar Marigayi Sheikh Jafar Mahmoud Adam Rahimahullah ya gabatar da
ita ne a ranar Alhamis 25 ga Rabi’ul Auwal,1428. wato dai-dai da 12th April, 2007.

Ya gabatar da wannan Nasihar a daren Juma’arda aka kashe shi, a wajen muhadarar da aka shirya a
masallacin Juma’a na Usman Bin Affan dake kofar Gadon kaya.Bayan dawowar sa daga garin Bauchi.

Ita wannan muhadarar malamai uku ne suka gabatar da ita daga cikin su akwai sheikh Dr Muhammad Sani Umar R/lemu da Malam Muhammad Aminu Ibrahim Daurawa da sheikh Muhammad Nazeefi Inuwa.

Wadannan sune malaman da suka gabatar da wannan muhadar. amma kasan cewar sheikh Jafar ya
dawo daga tafiya ne sai aka bashi minti goma yayi ta’aliki. Ga kuma yadda ta’alikin nasa ya ka sance :

Bayan Mallam ya yi godiya ga Allah, tare da yin salati ga manzon Allah salallahu alaihi wasallam, sannan ya yace “ya yan uwa musulmi abin da zan fada a nasiha ta ta karshe ’’ Allahu akbar wato wannan jumla ita Mallam ya fara bude maganarsa da ita, kamar yasan cewa washe gari juma’a zai riga mu gidan gaskiya, sai yaci gaba da cewa “Muji tsoran Allah, mu duka, muda zamuyi zabe’’ wato ya yi wannan Nasihar ne ana jajiberin
tsamiya na zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jihohi, Sannan ya ci gaba da cewa “ muda zamuyi zabe da kuma wadan da za’a zaba.

Asalin zaben nan malamai sunyi bayanin sa. Dukkan mutumin da zaka zaba, to ya zama cewa zaka zabe shi ne ba don maslahar ka ba
kai kadai, sai don maslahar al’umma gaba daya.

Akwai mutanen da suke fama da kuncin tunani, wadan da su tunanin su me zasu samu a
karkashin dan takara, sannan su ce a zabe shi; ko kuma me suka rasa suce kada a zabe shi.

Inda dan takara zai zo yabani naira
miliyan goma ni kadai a matsayi na na Ja’afar amma ya ha’inci alummar da yake wa mulki ta hanyar sauran bukatunsu, wadan da a asusun gwamnati akwai kudaden da za’a iya wadannan bukatu amma yaki yi, Ni kuma in
kalli miliyan goman nan ince ku zabe shi. To hakika na ci amanar kaina, kuma na ci amanar
ku talakawa bayin Allah, shi kuma shugaba na ha'ince shi.

Inda shugaba zai hana ni ko kwabo, amma ya zanto kudaden daya karba daga asusun gwamnatin tarayya ya aiwatar da su ta hanyar da ta dace. To wajibi na ne, in kiraye ku cewa ku zabe shi. Ba a dauki ma’aunin na ni me na samu ko me na rasa ba, masu irin
wannan sune wadan da suka jahilci Addini kuma suka jahilci rayuwa. Domin wannan shine yakai Nigeria cikin halin ka-ka-ni-ka-yi. Ganin in amfana ni kadai ko kuma a bude mana wata kafa mu yan tsiraru shi ke nan sai muyi shiru alhali mun san abin da shugaba yake yi ha’inci ne,amma sai mu daure masa gindi,hasali ma mu dinga kuruta jama’a cewa
dole ne su zabe shi, ba don komai ba sai don abin da bai taka kara ya karya ba.

To wannan kuntataccen tunani ne, kuma rashin hangen nesa ne rashin sanin ya kamata ne. Kullum zaka kalli me muka samu na ci gaba, ba me ni kadai na samu ba ’’
Allahu akbar sai malam ya kara da cewa“ ina kira ga ku matasa ku lura da yadda ake amfani da ku
’’malam ya buga wani misalin abin da ya gani yayin da yake dawowa daga tafiya sai yace “Da zu na shigo kano dab da lokacin sallar
maghriba kafin zuwana nan sai naga wadan da suke kanfen (campaign) wato da alamu anyi yawo da su cikin garine za su koma gida. Naga yara matasa an ciko su akan akorukura su kusan hamsin acikin motar nan kai da ganin su babu wanda ya yi sallar azahar ballan tana La’asa kuma galibin su da alamun sun bugu mota tana ta layi dasu suna ihu suna dauke da
hotuna suna sai wane sai wane kuma su wadan da suke bada kudi ayi hakan ciki babu ‘ya ‘yan su, nasu suna can, sun kai ‘ya ‘yan su
ma yan makarantu na cikin gida ko na waje.

Wannan shi ne hakikanin cin amanar al-umma, kai wannan shi ne haki kanin rashin mutunci, ka haukata ya yan talakawa bayan ka yin watar da su ka kuma ka jahiltar da su babu ilmin addini babu na rayuwa su kashe lokaci mai tsaho suna dauke da hotunan ka kan
kana son ka tsaya zabe a wani mataki na zabe. Akan abin da za’a basu wanda bai gaza Naira dari uku ko da hamsin ba.

Sannan mallam ya cigaba da nanata maganar sa ta farko inda yace “Hakika wannan ya ka mata ayi hattara, duk wanda zamu zaba, kada mu kalli me ya bamu, mu kalli dacewar sa da cancantar sa. Duk wanda zamu zaba ya kasance ya cancanta ko yabamu kudi ko bai bamu ba. Duk wanda bai cancanta ba to ko ya bamu fan taba sama to mu kadashi wannan shi ne gaskiyar lamari, amma idan ku ka tsaya da jahilci da kuntatacciyar
kwakwalwa ta ni an bani kaza ni naci kaza. To wannan tunani na ci bayane ba tunani ne na wanda yasan abin daya kamata ba’’.

Sai malam ya kara da cewa “Abin haushi da takaici hatta wadan su masu Magana da ya wun Addini akwai masu irin wannan kuntataccen tunani ubangiji ta’ala ya yi mana gamdakatar’’.

Allahu akbar wannan it ace Nasihar da malam ya yi ta karshe ga matasa kai dama dukkan wani mutum mai hankali.

Bayan an kammala wannan muhadarar da niyyar washe gari juma’a malam zai yi khudba akan zabe. Ranar juma’a da asubahi malam yana cikin sallah, ya karanta suratul Ma’arij aka samu wasu mutane miyagu azzalumai makiya Allah makiya san cigaban Addini, suka yi masa harbi da bindiga ba sau daya ba, ba sau biyu ba, kisan gilla inda suka harbe shi a kirjinsa na gefen hagu.

Anan muna rokon Allah ta’ala ya sa malam ya yi mutuwar shahada kuma ya karbi shahadar sa, Allah ya kyautata bayansa, ya sanya Albarka a cikin iyalansa da zurriyarsa. Wadanda suka aikata wannan aiki na ta'addanci a’ansa, su sani wannan tafarki da Mallam Jafar ya mutu akansa, kamar wata bishiya ce da bata tsiro bata tofo har sai mun shayar da ita da jinin jikinmu, wannan abu ko kadan bazai sanyamu mu yi rauni ba akan wannan tafarki. Allah ya daukaka Musulunci da Musulmai, ya Allah kada ka baiwa azzalumai dama domin su cutar da al’umma.

By: Yasir Ramadan Gwale

Like us on Facebook 

Tuesday, 3 December 2013

MAI HANKALI YI TUNANI! 3.

By: Baban Manar Alqasim

Yau za mu duba wani babban lamari ne ni da kai, domin a ranar Litini 29/02/0011 AH, Annabi ya fara rashin lafiya, bayan ya dawo daga janaza a maqabartar Baqi, a ranar Laraba wato kafin rasuwarsa da kwana Biyar, jikinsa ya dada daukan zafi matuqa, har ya yi ta wasiyya kan kar a bauta wa qabarinsa.

A ranar Alhamis, gabanin rasuwarsa da kwana Hudu, ranar ce cutar ta yi tsanani sosan gaske, kuma ranar ce ya ce a kawo takarda ya rubuta abin da in suka riqe shi ba za su 6ata ba har abada, Umar RA ya ce, akwai fa Qur'ani tare da ku, jikin ne ya matsa masa, a nan karatunmu na 3-4 zai fito in da Allah SW ya fadi a Qur'ani cewa addini ya cika ba saura, sannan in akwai lamarin Imamanci to sai Annabi ya qi fadi sai jiki ya yi tsanani zai rasu?

Annabi ya yi umurni da Abubakar RA ya jagoranci mutane sallah bayan Aliy RA yananan a gabansa, Mai hankali kar ka manta, ya jagoranci aikin haji a baya, yanzu ga shi Annabi SAW ya sake ba shi limanci a masallacinsa wanda ba wanda ya ta6a ba shi sai shi, Abubakar ne ya yi ta sallah har Annabi SAW ya bar duniya, bai canza wani ba.

A ranar Asabar, wato gabanin rasuwarsa da kwana Biyu yadan ji sauqi ya fita sallar Azahar alhali Abubakar RA yana limanci, sai ya nemi ya ja da baya, Annabi ya umurce shi ya tsaya a in da yake, sai ya riqa koyi da Annabi, wato mutum Biyu kenan a gaba, Annabi SAW da Abubakar RA, don Allah in da wani saqo da bai isar ba? Shin yanzu ba lokacin magana ba ne? Shin ina jarumtakar Aliy RA take idan har ba zai iya tsayawa kan abar Annabi ya fadi abin da aka aiko shi da shi ba? Ko dai ana zargin Annabi ne da tsoro, ta yanda ya qi fadin saqon Allah sabo da Umar ko Abubakar RA?

A ranar Lahadi, kafin rasuwar Annabi da kwana Daya, ya yi sadaka da dinari Bakwai, ya 'yanta bayinsa, ya yi kyauta da makaminsa amma bai rubuta wata wasiya ba, bai kuma fada ba, kenan zafin jikin ranar Alhamis ya tabbata, tun da yanzu ya murmure amma bai sake maganar ba.

A ranar qarshe Abubakar RA yana sallar Asuba da mutane Annabi ya yaye labulen windo daga dakin A'ishah ya leqo su ya yi murmushi, har mutane suka kusa fitunuwa a sallah sabo da murna suna zaton zai fito ne, Abubakar RA ya fara qoqarin dawowa baya, Annabi SAW ya nuna masa hannu cewa ya cika sallarsa, har hantsi ya daga Annabi ya bar duniya bayyi wata maganar wasiyya ba, yanzu Mai hankali me za ka ce?

Mai hankali ina so ka fahimci cewa, duk fa gabar da ake qoqari a shigo da ita tsakanin sahabbannan qarya ake yi,Qur'ani da sunna da marubutan shi'a na farko duk sun tabbatar da cewa sahabbai suna qaunar junansu, ba wata gaba da take tsakaninsu har suka bar duniya, Allah SW ya ce:
محمد رسول الله والذين معه أشداء على الكفار رحماء بينهم...
Muhammad dan saqon Allah ne, wadan da ke tare da shi masu tsananta wa kafurai ne da tausayawa a tsakaninsu.
Al Fat'hu 29

Za mu ga yadda Annabi ya auri 'yar Abubakar da Umar RA, Usman RA ya auri 'ya'yan Annabi guda Biyu, Aliy RA ya auri 'yar Annabi SAW, Umar RA ya auri 'yar Aliy RA duk wannan yana nuna qaunar da take tsakanin wadannan Khalifofin ne, domin auren Umar RA da 'yar Aliy RA bai kasance ba sai bayan rasuwan Annabi, kenan duk abin da ake fadi qarya ne kawai da canza tarihi.

Malaman shi'a suke cewa:
أنس رض قال قال لي النبي ص: انطلق فادع لي أبابكر وعمر وعثمان وطلحة والزبير وبعدد من الأنصار•قال: فانطلقت فدعوتهم له فلما أخذوا مجالسهم قال: ...إني أشهدكم أني قد زوجت فاطمة من علي على أربعمائةمثقال من فضة.
Anas RA ya ce Annabi SAW ya ce masa tafi ka kirawo Abubakar, Umar, Usman, Talhah, Zubair da wasu mutanen madina da dama. Ya ce sai na tafi na kirawo su, yayin da suka sami wuri suka zauna ya ce: Ku shaida cewa na aurar da Fatimah ga Aliy akan kwatankwacin azurfa 400.
Kashful Gumma 1/358. Bihar 43/119

Sannan hatta auren, lokacin da Aliyun RA bai da sadaki Annabi SAW ya ce sai dai ya sayar da sulkensa, haka ya dauka ya tafi wuri Usman RA, Usman ya kar6i sulken ya ba shi kudin, sannan ya mayarmasa da sulken a matsayin gudummuwarsa, da Aliy RA ya kawo kudin, Annabi SAW ya ba Abubakar RA kudin ya ce ya je ya siyo mata kayan daki.
Kashful Gumma 1/369. Bihar 43/130

Wadannan duk littafan shi'a ne suke bayyana qaunar da take tsakanin wadannan sahabban, na soyayya da qaunar juna, amma ba abin da suke koyar da dalibansu ba kenan, yanzu mu duba yadda Usman RA ya yi, a maimakon ya ba da kudin a matsayin sadaki a ce shi ya biya, sai ya sayi sulken da kudin da zai kai sadakin, don ya zama Aliy RA ya biya sadakin da guminsa, sannan ya mayar masa da sulkensa a matsayin gudummuwa, kuma ku duba wanda aka ba shi alhakin sayo kayan daki gaba daya, Abubakar ne RA, ku duba shedun da aka kira, wadannan su ne 'yan shi'a suke tsine musu kullun.

Mai hankali wadannan fa littafan shi'a ne, da za mu dauko littafan sunna ya kake zaton za mu bayyana abin? Shin me ya sa malaman shi'a ba sa koyar da dalibansu irin wadannan halayya da dabi'u masu dadi sai nuna gaba da tsinuwa ko da yaushe?

Like us on Facebook

MAI HANKALI YI TUNANI! 2.

By; Baban Manar Alqasim

بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل وسلم على نبيك محمد وآله وصحبه وسلم.

Mai hankali dan taimake ni duba wannan lamarin: Annabi SAW shi ne da kansa yake wakiltar Sahabbansa gaba Daya a duk aikin Haji wanda shi ma ginshiqi ne daga shika-shikan muslunci, amma a shekara ta Tara bayan Hijira sai ya tura Abubakar RA da ya na'ibance shi, ya jagoranci jama'a, a Daya daga cikin rukunan muslunci wanda dukkan musulmai za su dawo qarqashinsa ne, shi ne mai umurni da hani a matsayin jagora, har sai da ayar warware duk ittafaqin da musulmai suka rattaba hannu ta sauka, wace Annabi SAW ya tura Aliy RA da ita da cewa ya bi Abubakar RA ya karanta wa musulmai a matsayinsa na dan saqo.

A wannan shekarar, Abubakar ya zartar da hukuncin cewa babu sauran bautar gumaka a yankin Larabawa gaba Daya, tun daga wannan ranar, shin hankali zai dauka a ce kuma ya riqa bauta musu a 6oye, sannan Allah bai gaya wa Annabinsa ba, har ya jagoranci mutane a irin wannan matsayi na jagorancin duniya? Wani irin qwaqwalwa ce wannan? A wannan lokacin ne fa Abubakar RA ya hana duk wani mushriki dawafi, ta ina za a sifanta shi da wannan in an so adalci?

A shekara ta Goma Annabi ya yi Hajjin ban kwana mai ban tausayi, wanda bayansa ba a sake yi da shi ba, sai Abubakar RA ya ci gaba da jagorantar aikin haji a matsayinsa na Khalifa bayan Annabi, kenan kamar Annabin ya koyar da shi ne tare da nuna wa duniya matsayinsa a harkar addini, a wannan lokaci ne Annabi ya yi bayani dalla-dalla game da abubuwan da suka shafi addini manya da qanana, amma sam bai yi maganar Imama ko Wilaya ko Wasiyya da 'yan shi'a suke zaluntar muslunci da shi ba, su ma ba su yi da'awar cewa ya yi ba, har ayar qarshe ta sauka wa Annabi cewa:
اليوم أكملت لكم دينكم وأتممت عليكم نعمتي ورضيت لكم الإسلام دينا.
A yau dinnan na kammala muku addininku, na cika muku ni'imata, na amince muku cewa muslunci shi ne kadai addini.

Mas'aloli masu mahimmanci su ne: In dai har akwai maganar wasiyya, Annabi bai riga ya isar ba bayan duk Annabawa sun san da ita, ta ya Allah SW zai saukar da cewa addini ya cika? Musulmi ba zai ce Allah SW bai san cewa Annabi bai isar da wasiyya ba, matuqar akwai ta. To sai dai a ce ai lokacin maganar wasicin ba ta zo ba, da Annabi ya isar a wurin, wannan ya sa6a wa aqidar shi'a gaba Daya, don Annabi wai tun aiko shi yana sane da khalifancin Aliy RA, bal duk manzanni ma sun sani, to a nan wa za a zarga? Kowanne zargi a ciki kafurci ne.

Dan uwa musulmi, baka da bukatar wahal da kanka, ko ba ka da ilimi ka san cewa, maganar wasicinnan dama ce da za a zargi Annabi SAW da rashin isar da saqo gaba Daya, don kuma bai ta6a maganar wasici ba ko khalifancin Aliy RA, ta ya sai ya zo rasuwa ne zai yi???

Mai hankali dan saurare ni kadan! A sama na  kawo ayar da take tabbatar da cewa Annabi Muhammad SAW ya isar da saqo:
اليوم أكملت لكم دينكم وأتممت عليكم نعمتي ورضيت لكم الإسلام دينا.
A yau dinnan na kammala muku addininku. Na cika muku ni'imata, na amince muku cewa muslunci shi ne kadai addini.
Ma'ida aya ta 3

Wannan ya nuna babu wani zancen Imama wanda Annabi bai isar ba, sai dai in za a zarge shi da 6oye saqon da Allah ya yi masa, ko a qaryata ayar Qur'ani, koda yake kai mai hankali ka san cewa ba yadda za a yi Annabi SA ya 6oye wani abu bai isar ba a matsayin manzo kuma Allah SW ya qyale shi, to mu ahlus sunna mun yi imani cewa Annabi ya isar da duk saqon da aka yi masa, maganar imamanci da bai fadi ba dama ba muslunci ba ne da ya isar.

Khumaini yake cewa:
وواضح أن النبي لو كان قد بلغ بأمر الإمامة طبقا لما أمر به الله وبذل المساعي في هذا المجال لما نشبت في البلدان الإسلامية كل هذه الاختلافات والمشاهنات والمعارك ولما ظهرت ثمة خلافات في أصول الدين وفروعه.
A sarari yake cewa da Annabi ya isar da lamarin Imama kamar yadda Allah ya umurce shi, kuma ya zage dantse a kan haka, da duk wadannan sa6anin da tashin-tashina da rikice-rikicen da suke faruwa a qasashen muslunci ba su faru ba, kuma da ba a sami wani sa6ani a Tauhidi da Fiqihu ba.
Kashful Asrar na Khumaini.

Ya fito sarari kenan dama Annabi suke so su zarga da cewa bai isar da saqon da Allah ya yi masa ba, in kuwa za su yi wa Annabi haka, haqiqa Abubakar da Umar RA ba tsira za su yi ba, don sun zarge su da hana wasiya, mai hankali kar ka yi zaton Annabi ne kadai suke zargi a'a hatta sauran Annabawan dubi abin da Khumaini yake cewa a wata huduba da ya yi ta tunawa da haihuwar Mahadi a ranar 15 Sha'aban 1400 AH:

لقد جاء الأنبياء جميعا من أجل إرساء قواعد العدالة في العالم لكنهم لم ينجوا حتى النبي محمد خاتم الأنبياء الذي جاء لإصلاح البشرية وتنفيذ العدالة لم ينجح في ذلك.
Annabawa gaba dayansu sun zo ne don saka ginshiqai na adalci a bayan qasa, sai dai sun gaza yin hakan, hatta Muhannad, cikamakon Annabawa da ya zo domin gyara dan adam da zartar da adalci ya gaza yin hakan.
Ka duba Nahaju Khumainiy p46

Wannan ya nuna cewa suna da tabbacin cewa Annabi bai bar wata wasiyya da zata tabbatar da cewa Aliy RA shi ne khalifa bayan Annabi ba, to mai hankali wanda zai furta irin wandannan kalaman ga Annabin rahama kana ganin zai qyale sahabbansa?

ME HANKALI YI TUNANI

By: Baban Manar Alkhasim.

بسم الله الرحمن الرحيم

اللهم صل وسلم على محمد وآله وصحبه ومن تبعهم بالإحسان الى يوم الدين.

'Yan uwana musulmi, wannan sabon darasi ne, me yiwuwa ya dan bambanta da sauran kadan ta 6angaren aiki da hakali, ina buqatarka dan uwa, wanda Allah SW ya halicce ka da hankali ya kuma ba ka daman neman ilimi don ya bambanta ka da sauran dabbobi, da ka ba ni hankalinka kadan don mu duba inda gaskiyar take.

Lokacin da Allah SW ya yi niyyar aiko Annabi SAW duk duniya ta saki addininta, Banu Isra'ila wasu sun bar koyarwar Annabi Musa sun bi Yahudanci, Nasaran da suka kar6i addinin Annabi Isa AS suma sun canja littafin kamar dai yadda Allah SW yake cewa:
يحرفون كلم عن مواضعه.
Suna canja kalmomi daga asalin yadda suke.

Don haka zuwan Annabi SAW bai tsaya ga Larabawa ba kadai, wadan da suka saki addinin Annabi Ibrahim wato muslunci, suka dauki sabon addinin da Amr bn Lu'ay ya zo musu da shi daga qasashen Sham, har duniya gaba daya dole ta karyo kai zuwa ga Annabi Muhammad domin komowa zuwa ga muslunci,

Sai Allah SW ya turo Annabi SAW da saqo, shi kadai ne bai hada shi da kowa ba, ba kuma wani manzo kusa da zamaninsa a duk al'ummar duniya, ba kamar Banu Isra'ila ba da Annabawan ke bibiyar juna ko su zo a lokaci guda, Annabi Ibrahim da 'ya'yansa Biyu Isma'eel da Is'haq da jikansa Ya'qub da tatta6a kunnensa Yusuf AS duk manzanni ne bayansu kuma, Musa, Haroun, Shu'aib da Khidir duk zamani Daya suka yi da Thulkifl da Yusha' AS, sai kuma Dawoud da dansa Suleiman AS, suka yi zamani Daya, Zakariyya da dansa Yahya da Isa AS duk zamani Daya suka yi, Annabi SAW shi kadai ya zo shi Daya zuwa ga duniya gaba Daya ba kamar wadancan manzanni da aka aiko su zuwa ga Banu Isra'ila kadai ba.

Annabi yana kar6an wannan saqo Abubakar RA ya muslunta ba tare da wa'azi ko jinjiki ba, ya kar6i addinin ya yi watsi da wanda tun yana yaro yake ciki, haka ya lazimci Annabi SAW har Qur'ani ya sifanta shi da:
ثاني اثنين إذهما في الغار إذ يقول لصاحبه لا تحزن إن الله معنا.
Dayan mutum Biyu yayin da suke cikin kogo, lokacin da yake cewa abokinsa kada ka damu haqiqa Allah yana tare da mu.
Abubakar ya yi dace da sahibantan Annabi SAW a cikin lamarin risala, in da Annabi ya dauke shi suka bar garin Makka tare.

Abin kula a nan, me ya sa Annabi ya dauke shi, mu ahlus sunna mun ce, ba bu kamarsa a wannan lokacin, kuma shi ne ya cancanci wannan matsayin sai Annabi ya za6o shi, Allah SW ba zai bar Annabi ya yi kuskuren za6en wanda zai taimake shi isar da saqo ba, mun yi Imanin cewa Allah yana sane da Abubakar RA tun kafin ya halicce shi, da abin da zai yi har mutuwarsa don haka ya bar Annabinsa da shi.

Mai hankali zan so ka taya ni wannan hukuncin, saninka ne cewa Annabi SAW ya yi niyyar fita zuwa Madina, wanda wannan tafiya mai matuqar mahimmanci ce a tarihi da addini, tafiya ce da take nuna tashin muslunci a hukumance daga mahaifar Annabi Makka zuwa Madina, mai ya sa bai dauki Aliy RA ba sun tafi tare tunda yana da masaniyar cewa shi ne Khalifansa a bayansa?

Mai yiwuwa amsar ta zama cewa: Aliy RA ya riqi wani matsayi ne mai girma, mai matuqar wahala da hatsari, na fuskantar mutuwa daga abokan gaba, ta yadda ya kwanta a makwancin Annabi SAW, wanda da kafurai sun zo da sun kashe shi, sabo da shi kadai ne ba zai iya fuskantar garin Makka gaba daya ba.

To ma iya cewa Annabi ya kai khalifansa in da za a kashe shi kenan don ya ba Abubakar RA daman hawa khilafa? Amsar za ta iya zama a'a ai shi sadauki ne kuma Annabin yana sane da cewa kafuran ba su isa su ta6a shi ba Allah zai kare shi.

In dai amsar ta fito a haka to ba maganar tsoro ko hatsari, Allah yana tare da shi zai kare shi, amma tun da ya zama Annabi bai fita a fili zuwa Madina ba, sai da daddare kuma a bayan idon jama'a, har suka shiga kogon dutse, lallai wurin akwai hatsari, nan ne ya kamata sadauki ya yi aiki, to sai Annabi ya bar Aliy RA a wurin da ya san babu hatsari, duk da jarumtarsa da ake fadi, ya dauki Abubakar suka fita, sabo da saninsa da kuma amincewa da qudurarsa, tun da Allah ya umurce shi da fita ba zai bar Annabinsa ya yi kuskure wajen daukan abokin tafiya a wuri mai mahimmanci irin wannan ba.

Idan muka lura da kyau za mu ga cewa Annabi SAW cewa ya yi لا تحزن. "Kar ka damu" ba. لا تخف ba wato "kar ka ji tsoro" Abubakar RA duban halin da Annabi yake ciki ne shi ya sa ya ce kada ka damu Allah zai tsare mu, ya san ba tsoro a zuciyarsa da ya ce kada ka ji tsoro.

Haka Annabi SAW ya lazimci Abubakar RA har rasuwarsa, Qur'ani bai bar wani munafuki ba sai da ya tona shi, wajibin Annabi ne kuwa ya isar da saqo, ya fallasa duk wani munafuki.

Amma Annabi sai ya auri 'yar Abubakar RA wato A'ishah RA, alaqar ta dada qarfi, bayan rasuwar Annabi SAW, Abubakar ya yaqi 'yan ridda dole suka shiga muslunci, kenan hankali ba zai dauka ba a ce shi ma ya yi ridda kuma yake yaqin 'yan ridda, sannan ya kuma fara bude qasashen shi'a har mutuwa ta same shi, kenan bai bar abin da Annabi SAW ya dauko ba. Za mu duba maganar wasiyya da kai, kai kuma sai ka yi tunani.

A kan wannan ga6ar za mu ci gaba InshaAllah.

Like us on Facebook

Sunday, 1 December 2013

The Miser and the Angel of Death

By Abubakar Hassan

A miser had accumulated, by effort, trade and lending, three hunderd thousand dinars. He had lands and buildings, and all kinds of wealth. He then decided that he would spend a year in enjoyment, living comfortably, and then decide as what his future should be.

But, almost as soon as he had stopped amassing money the Angel of Death appeared before him, to take his life away.

The miser tried, by every argument which he could muster, to dissuade the Angel, who seemed, however, adament. Then the man said: "Grant me but three more days and I will give you one-third of my possessions."

The angel refused, and pulled again at the miser's life, tugging to take it away.

Then the man said:

"If you only allow me two more days on earth, I will give you two hundred thousand dinars from my store."

But the Angel would not listen to him. And the Angel even refused to give the man a solitary extra day for all his three hundred thousand pieces.

The the miser said:

"Please, then, give me just time enough to write one little thing down."

This time the Angel allowed him this single concession, and the man wrote, with his own blood:

"Man, make use of your life. I could not buy one hour for three hundred thousand dinars. Make sure that you realize the value of your time."

Source: Obtained from the book "The Way of the Sufi" by Idries Shah.

Like us on Facebook

Friday, 29 November 2013

Dua when waking up from sleep

*BismillahirRah manirRaheem*

Assalam o Alaikum Wa rahmathullahiWabarakatuhu wa maghfiratuhu Dear Brothers and sisters ALHAMDO LILLAH, SUBAH AL-NOOR. plz recite morning dua if u forgot.

'Alhamdolillah hillazi ah'yana ba'dama amatana wa ilaihin'nushur'

All praise for Allah swt who gave life after taking it. Unto him we are back from this world..

Like my page by clicking on this name IslamInNageria or this name Islam4all
•*´¨`*•. ¸¸.• •*´¨`*•.

Dua for entering toilet

بِسْمِ اللَّهِ. اللَّهُـمَّ إِنِّي أَعُـوذُ بِـكَ مِـنَ الْخُـبْثِ وَالْخَبَائِثِ

Bismillaahi. Allaahumma 'innee 'a'oothu bika minal-khubthi walkhabaa'ith. In the Name of Allah. O Allah, I seek protection in You from the male and female unclean spirits.

Like us on Facebook

Thursday, 28 November 2013

MARASA AURE( MAZA da MATA )

MARASA AURE( MAZA da MATA )Wa iyazu billah
MU BUDE KUNNE MUJI

akwai wani bala'i wanda ya kunno ma
al'ummar musulmi kai... Ita
wannan musibah ta fi aukuwa ne ga marasa
aure...

Zaka iske namiji ko mace a duk
sa'ar da sha'awarsu ta motsa sai
su rika wasa da al'aurar su har
sha'awar tasu ta kwanta (fitar da
maniyyi) wannan shi ake kira da suna Istimna'i
ko masterbation a
turance.....

Ganin haka yasa nayi
farautar
fatawa daga
wasu malamai a kan ko mene ne
hukuncin abun a musulunci

sai malam ya ce
''Duk mai yin
ISTIMNA
(MASTURBATION) Mace ko
Namiji, idan har bai tuba ya daina
ba, ko idan har bata tuba ta daina
ba, babu mamaki daya daga cikin cututtukan
nan guda goma (10) ya same ta/
SHI, ko
kuma
ma sama da ciwo daya ya sameta,
ko ya sameshi. ALLAH YA KAREMU,
AMIN.

1-Yana Rage karfin ido
2-Rage karfin namiji ko mace a
wajen kwanciya, kanaso ka biya
bukata amma ba dama.
3-Yana shafar lafiyar jijiyoyin da
suke da ala’ka da fitar maniyyi, ko
yasa duk
lokacin da zakayi fitsari sai kaji
kamar ana tsira allura a cikin gabanka (zafi
sosai)
4- Yana
haifar da wani irin ciwo a
cikin mutum
5- Yana shafar lafiyar ‘ya’yan maraina, kuma
ya kankantar da
gaban namiji
ya koma kamar na karamin yaro.
6- Yana sa
saurin fitar
maniyyi a lokacin saduwa
7- Yana kawo ciwon
kashin
gadonbaya
8- Yana rage kaurin maniyyi,
wanda kuma zai iya shafar lafiyar
abin da za a haifa, koma ya hana
haihuwar gabadaya
9-Yana sa kuraje a jikin
mutum
10-Yana rage kaifin
kwakwalwa

MAI NEMAN KARIN BAYANI YA DUBA CIKIN
LITTAFIN FATAWA
NA
SHEKH BN BAZ DA SHEKH
UTHAIMIN
DA KUMA SHEKH BN JUBAIRU,
JUZ’I NA BIYU SHAFI NA 132-133''

Bayan malam ya kare fatawar sa
sai muka tuntubi wani mai kula
da Lafiya shima ya ce; ''kasan
maniyyin da ke fita kadan ne,
sabili da ba a ainihin saduwa ne maniyyin ya
fita ba, so saura zai
rage kuma zai yi ta taruwa a
mararsa da haka sai ya ja masa
illoli ta fuskar Lafiyar sa. Misali duk
mai yin wannan abuzaka iske
yana shan wahala ko yaya ne wajen fitsari.

To ina anfanin
wannan'' To yan'uwana sai mu
dage mu yi aure ko mu yawaita
azumin nafila da karatun alqur'ani
da kasancewa da muminan
abokai da gujewa fasikan abokanai....

Sannan mu ji tsoron
Allah mu guji kallace kallacen
banza da wofi.
Allah ya kara kare wadanda basu
aikata
wannan mummunan bala'in su kuwa
wadanda keyi Allah (s.w.t) ya
shirye su su
daina.